Hukumar zaben Nigeria tace tana bukatar karin lokaci domin rajistan masu zaben watan afrilu idan Allah ya kaimu. A yau Laraba shugaban hukumar Attahiru Jega ya bukaci Majalisar dattijai data yiwa dokar zabe gyara domin a kara lokacin yin rajistan masu zabe.
Jega yace karin lokacin zai baiwa jami’ai damar yiwa dukkan wadanda suka cancanci zabe rajista. An dai kiyasta cewa akwai kimamin mutane miliyan saba’in da suka cancanci zabe a Nigeria, kasar data fi kowace kasa a nahiyar Afrika yawan jama’a.
Muna da karin bayani akan wannan labari bayan labarun duniya. A wani labarin kuma yanzu haka manyan shugabanin kamfanin mai na Shell suna can kotu a birnin Hague suna kare aiyukan da suke gudanar a Nigeria inda yan kishin kasa suka ce kamfani yana keta hakkin jama’a da jawo gurbacewar yanayi.
Kamfani Shell yace kashi saba’in daga cikin dari na matsalar yoyon mai suna faruwa ne a saboda mazauna yankin ne kan huda bututun mai domin su saci mai.