Uwar Jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta bayyana shirin sake zaben fidda ‘yan takarar gwamna a jihohin Kogi da kano.
Cikin sanarwa ga manema labarai da kakakin jam’iyyar Parfessa Rufa’I Alkali ya sanyawa hanu za’a sake zabubbukan ne a ranar talata 25 ga wata nan.
Babban kwamitin gudanarwar Jam’iyyar, yace ya yi nazarin kararrakin da ‘yan takara a duk fadin Najeriya suka gabatar,ya kuma duba rahoton kwamitin daukaka kara,da kuma rahoton hukumar zabe wacce ta sa ido a zabubbukan fidda ‘yan takara.
Domin haka Jam’iyyar zata sake zabubbukan fidda ‘yan takarar majalisar dattijai a wasu mazabu cikin jihohin Delta,Oyo,Sokoto,Bauchi,Adamawa,da Taraba da kuma Kogi.
A Delta za'a sake zaben ne na mazabar majalisar dattijai,Delta ta tsakiya. A jihar oyo, za'a yi zaben ne na mazabar Oyo ta tsakiya. A Sokoto, za'a yi zaben ne na mazabar Sokoto ta Gabas.A Bauchi,za'a sake zaben ne domin mazabar Bauchi ta Arewa. A Taraba, za'a sake zaben ne na mazabar Taraba ta tsakiya. A Adamawa za'a sake zabubbukan ne na mazabun Adamawa ta Kudu,da kuma ta Arewa. A Kogi kuma,za'a sake zabubbukan ne na mazabunKogi ta Tsakiya,Gabas,da kuma Yamma.
Za'a gudanar da zabubbukan ne ranar laraba 26 ga watan janairu,kuma sai 'yan takara da aka riga aka tantance,kuma suka shiga zaben da ya wuce ne zasu yi takara a wan nan zubin.