Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Zargin Masar Da Kin Baiwa ‘Yan Kasar Da Aka Dauko Daga Sudan Damar Shiga


'Yan kasar Birtaniya suna ficewa daga Sudan
'Yan kasar Birtaniya suna ficewa daga Sudan

Gwamnatin Najeriya ta zargi kasar Masar da kawo cikas a yunkurin gwamnati na kwashe 'yan Najeriya da ke Sudan inda ake fama da tashin hankali.

A yayin da Najeriya da sauran kasashen duniya ke ta kokarin fitar da 'yan kasar daga Sudan inda rikici yaki ci-yaki cinyewa.

Gwamnatin Najeriya tace hukumomin kasar Masar sun ki baiwa 'yan kasashe daban-daban da suka kai akalla dubu bakwai (7000) wadanda suka hada da ‘yan Najeriya, damar shiga kasar bayan isarsu iyakar Sudan da Masar jiya Alhamis.

Shugabar Hukumar kula da 'yan Najeriya dake kasashen waje ta Najeriya NIDCOM Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana haka a wata rubutacciyar sanarwa i da ta fitar yau Juma’a.

'Yan kasar Sudan da ke gudun hijira a Chadi
'Yan kasar Sudan da ke gudun hijira a Chadi

A cikin sanarwar, Madam Abike ta bayyana cewa, “Najeriya na kira ga dukkan wadanda abin ya shafa kan shige da fice a iyakokin Sudan, da su baiwa ‘yan kasashe da dama harda ‘yan Najeriya da suka kai dubu bakwai damar shiga don isa inda suke son isa.”

Ta kara da cewa, Ofishin Jakadancin Najeriya dake Masar na iya kokarinsa don ganin ‘yan Najeriya sun shiga kasar ta Masar, yadda za a iya dauko su zuwa Najeriya, amma hukumomin kasar Masar sun yi kememe suna cewa, dole sai kowanne dan Afrika da zai shiga kasar ya mallaki izinin shiga kasar wato visa sannan zai sami damar shiga don wucewa zuwa kasarsa.

Shaguna da aka rurrusa a wata kasuwa da ke Arewacin birnin Khartoum
Shaguna da aka rurrusa a wata kasuwa da ke Arewacin birnin Khartoum

Shugabar Hukumar kula da 'yan Najeriya dake kasashen waje ta Najeriya ta kuma yi kira ga hukumomin kasar Masar a sanarwar inda ta ce, “Muna rokon hukumomi Masar dasu baiwa wadannan matafiya dake cikin dimuwa damar shiga don su sami damar wucewa kasashen su dake nahiyar Afrika.”

~Alhassan Bala~

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG