Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAJERIYA: Kwanan nan Za'a Fara Cafke duk Wadanda Suka Wawure Dukiyar Kasar


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A cigaba da kokarin canza alkiblar kasar shugaban Najeriya yace dole a cafke duk wadanda suka wawure arzikin kasar a kuma hukuntasu idan ana son kasar ta cigaba

Yau Talata a Abuja shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sanar cewa nan ba da dadewa ba za'a fara tuhumar wadanda suka wawure arzikin kasar.

Ya sanarda hakan ne yayin da 'yan kwamitin wanzar da zaman lafiya a karkashin jagorancin Janar Abubakar Adulsalami suka kai masa ziyara a fadarsa ta Aso Villa.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta dukufa kain da nain tayi duk abun da zata iya yi cikin ikonta ta yaki cin hanci da rashawa da rashin aiki da kuma rashin tsaro da suka yiwa Najeriya katutu.

Dole ne Najeriya ta karya lagwan cin hanci da rashawa kafin ta kama hanyar cigaba. Shugaban ya hada da cewa gwamnatinsa tana nan tana tara bayanai dangane da kadarorin da aka sace da yadda aka sacesu kafin ta ftar da sunayaen wadanda suka aikata aika aikar da kuma gurfanar dasu.

Shugaba Buhari ya fadawa Janar Abdulsalami da 'yan tawagarsa cewa gwamnatin yarayya ta yanzu a karkashin shugabancinsa ba wai zata ce a mayar da kaddarorin da aka sata ba ne kawai wadanda aka kai aka boye a bankunan kasashen waje, zata tabbatar wanda suka kunkuma satar an gurfanar dasu gaban kuliya a Najeriya.

Shugaba Buhari yace yayinda gwamnatinsa ke kokarin warware matsalolin da ta gada daga gwamnatin da ta shude ta fara sauya yadda take tattara kudaden shiga tare da kirkiro sabbin hanyoyi.

Shugaban yace daga yanzu gwamnati zata yi anfani da baitulmali daya ne tak. Wato duk kudaden gwamnati asusu daya zasu shiga sboda tabbatar da gaskiya akan yadda aka tara kudaden da kuma tabbatar da adalci akan yadda ake anfani dasu

Kasar ta gurbace. Yawancin ma'aikatunmu sun sukurkuce hatta ma sojojinmu wadanda a da sun yi fice a kasashen duniya amma su ma ba'a barsu ba. Amma muna wani abu a kai. Sojojinmu sun soma farfadowa inji shugaba Buhari.

Shugaba Buhari yace lokacin da yake ministan ma'aikatar man fetur a karkashin gwamnatin Obasanjo bashi da izinin fita kasar waje sai ya gabatar da takardunsa gaban majalisar zartaswa saboda a amince masa da kudaden da zai yi tafiya dasu. Amma yanzu fa kowa abun da ya ga dama yake yi.

Shuagaban yace dalili ke nan tsaro ya tabarbare. Tattalin arziki ya sukurkuce kana kasar kuma ta shiga halin lahaulawalakawati.

Shugaban ya sake jaddada cewa nan da 'yan makwanni 'yan Najeriya zasu san wadanda suka zalunci kasar.

XS
SM
MD
LG