Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamun Ludayin Buhari


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Paul Biya na Kamaru.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Paul Biya na Kamaru.

Mayarwa juna martani na cigaba tsakanin jam’iyyar APC da ta amshi mulki, da PDP da mulki ya sullube mata, kan kamun ludayin gwamnatin Buhari.

Har yanzu kakakin PDP Oliseh Metuh da mukarrabansa ke cewa an saka shi saboda kare muradun PDP na nuna APC da Shugaba Buhari sun kasa seta mulkin Najeriya.

A ‘yan watanni biyu da kwanaki tun amsar mulkin ‘yan rajin kare APC irin su injina Kailani Muhammad na gani Buharin ya fara kawo sauyi “in aka samu mutane na kwarai, babu yadda za’a yi a sayar da kayan gwamnati”

A nasa bangaren, tsohon mai taimaka wa shugaba Jonathan kan masarautu Barayan Bauchi Sunusi BabanTanko na gani Buhari zai iya nasara amma sai ya kaucewa binciken jami’an gwamnatin da ta shude.

“Ya dena duba baya, yana bawa kansa wahala. In yace dole sai kowa an bincike shi, duk wanda ka sani a kasar nan, babu wanda ba za’a kama ba.”

Me masu sharhi kan al-amuran yau da kullum ke cewa kan mulkin Buhari? Nasiru Gambo Malumfashi yace “ko ina yanzu, sakon canjin nan ya kai. Yanzu duk inda zaka je, yanayin yadda ake abubuwa ya canza.”

Da yawa dai sun yi bakan game da sharhi kan gwamnatin Buhari wata kila har sai bayan kwanaki dari kafin nan Buhari ya nada Ministoci. Haka kuma wasu basu san ta ind Buharin zai bullo musu ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG