Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Ya Sa Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya ta Fadi?


Kasuwar hannun jari
Kasuwar hannun jari

Cikin watan da ya gabata kasuwar hadahadar saye da sayar da hannun jarin kamfanoni ta Najeriya ta yi asarar kudi fiye da nera tiriliyon daya to ko me ya jawo haka?

Alhaji Kasumu Garba Kurfi wanda yake da kamfanin hadahadar saye da sayar da hannun jari ya zanta da Muryar Amurka akan musabbabin faduwar kasuwar.

Lokacin da aka bayyana shugaba Muhammad Buhari a matsayin wanda ya lashen zaben shugaban kasa kasuwar tayi wani tashin goron zabi. A rana daya ta samu ribar kusan nera tiriliyon guda.

Bayan da aka rantsar dashi kasuwa na tsammanin abubuwa zasu daga to amma hakan bai faru ba. Abu na farko da shugaban ya fada na cewa ba zai nada ministoci ba sai watan tara ya karyawa masu saka jari gwiwa. Wannan kalamin nasa ya sa kasuwar na tababan manufarsa da irin alkiblar da yake dashi akan abubuwan da suka shafi tattalin arziki.

Tunda bashi da ministoci bai kuma zakulo wadanda zasu bashi shawara ba mutane sun sami kansu cikin duhu.Saboda haka kasuwar sai ta soma yin kasa.

Abu na biye shi ne tabbacin da gwamnan babban bankin Najeriya wato Central Bank ko CBN ya bayar na cewa ba zasu kara rage karfin nera ba.Amma kuma a kasuwar bayan fagge ana sayar da dalar Amurka nera dari biyu da talatin ko fiye da haka.

Saboda rashin tabbas inda nera ta tsaya akan sayen dala sai masu shigowa da jari daga kasashen waje suka yi dari-dari da shigowa da kudi. Basu ga dalilin da zasu shigo da dala ba CBN ta canza masu akan nera dari biyu alhali kuwa kasuwar bayan fage na sayan dala dari biyu da talatin ko fiye ma. Wannan lamarin ne ya jawowa kasuwar hasara.

Amma motsin da gwamnati ta fara yi yana taimakawa wurin farfado da kasuwar. Misali nada sabon shugaban NNPC wadda ita ce cibiyar tattalin arzikin Najeriya ya sa kasuwar ta tashi.

Faduwar kasuwar hannun jari ba attajirai kawai take shafa ba. Tana shafan mai karamin karfi ta fuska biyu. Makon jiya hannun jarin Gurrantee Trust Bank nera 22 amma wannan makon ya tashi zuwa nera 25 da 'yan kai. Ke nan mai karamin karfi idan yana da hannun jarin wannan bankin dubu daya ya samu ribar nera dubu uku ke nan. To shi ma kasuwar ta shafeshi.

Dangane da kayan masarufi yadda mutum ya sayi dala haka zai sayar da kayan da talaka ke anfani dasu na yau da kullum. A tuna kusan komi da ake anfani dasu ana kawosu ne daga kasashen waje. Wadanda akesarafawa cikin gida kayan da ake anfani dasu daga waje ake kawosu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG