A yau alhamis aka yi wata ganawa a tsakanin shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya da mukaddashin firayim ministan kasar Kamaru, Ahmadou Ali, wanda yayi tattaki zuwa Abuja dauke da wani sako na musamman daga shugaba Paul Biya.
A cikin wannan sakon, shugaba Biya na Kamaru ya gayyaci shugaban na Najeriya domin su gudanar da wani gagarumin taro na shata yadda zasu tabbatar da tsaron bakin iyakarsu ta kasa da kuma ta ruwa, da nufin inganta harkokin tsaron yankin Afirka ta Yamma.
Wannan yana zuwa a bayan da Najeriya ta ayyana kafa dokar-ta-baci a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe a yankin arewa maso gabas, inda Najeriya ta yi iyaka da kasar ta Kamaru, da kuma kasashen Chadi da Nijar.
Kamaru dai ta rufe bakin iyakokinta ta kasa da Najeriya a bayan ayyana dokar-ta-bacin, domin tabbatar da cewa 'yan bindigar da ake farauta ba su tsallaka iyaka suka sulale cikin Kamaru ba.
Wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa, ya tattauna da shugaban Kwamitin Harkokin Cikin Gida na Majalisar Wakilan Tarayya ta Najeriya, Alhaji Umar Bature, kan wannan hadin kan da ake shirin kullawa a tsakanin Najeriya da Kamaru.