Wannan dokar hana fitar zata fara aiki daga yau laraba, 16 ga watan Mayu.
Kakakin birged ta 23 ta sojojin Najeriya a Yola, Leftana Jaafar Mohammed Nuhu, shine ya bayyana wannan a lokacin da yake bayani ga 'yan jarida na irin matakan da suka fara dauka dangane da dokar-ta-bacin da gwamnatin tarayya ta kafa a wasu jihohi uku na yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Leftana Jaafar Nuhu ya bukcai jama'a da su bi doka, su kuma yi aiki da dukkan umurnin da hukumomi zasu bayar domin a samu nasarar maido da zaman lafiya cikin kankanin lokaci.
A halin da ake ciki kuma, kungiyoyin al'umma a Jihar Adamawa sun fara gangamin fadakar da jama'a irin matakan da ya kamata su dauka domin tabbatar da cewa ba su cutu ba a karkashin wannan dokar ta bacin.
Ibrahim Abdulaziz ya aiko da cikakken bayani game da wadannan matakai na hukuma, da abubuwan da kungiyoyin al'umma keyi da kuma ra'ayoyin da jama'a suke bayyanawa na halin da suka samu kansu ciki.