WASHINGTON, DC —
Tsohon shugaban Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana goyon bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na shawo kan tashe tashen hankali a jihohi uku na arewa maso gabashin kasar.
A cikin hirarshi da manema labarai Janar Babangida yace daukar matakin kare mutumcin kasa ko ta wace hanya abu ne da ya dace. Ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya su marawa shugabanni baya a yunkurin wanzar da zaman lafiya domin ci gaban kasa baki daya.
Janar Babangida ya bayyana haka ne a cikin hirarsu da manema labarai a garin Minna fadar gwamnatin jihar Naija.