Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tura Karin Sojoji Zuwa Jihohi 3 A Najeriya


Jaridu a Najeriya sun ce sojoji dubu 2 tare da jiragen saman yaki sun isa Jihar Borno, yayin da wasu ke isa jihohin Yobe da Adamawa

An tura karin sojoji masu yawa zuwa wasu jihohi uku na arewacin Najeriya, inda a jiya talata shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana kafa dokar-ta-baci a wani martani ga 'yan kishin Islama dake tawaye.

Jaridun Najeriya sun buga rahotannin cewa sojoji kimanin dubu 2 tare da jiragen saman yaki sun isa Jihar Borno, yayin da shaidu suka ce sun ga dimbin sojoji su na kwarara zuwa cikin jihohin Yobe da Adamawa masu makwabtaka da Borno.

Jiya talata, shugaba Jonathan yace 'yan tawaye sun kame wasu sassan Jihar Borno, ya kuma umurci hukumomin tsaron kasar da su dauki dukkan matakan da suka kamata domin kawo karshen wannan tawaye a yankin.

Kungiyar Boko Haram mai cibiya a Jihar Borno, ta fara yakar gwamnatin Najeriya tun shekarar 2009. Mutumin da ake ikirarin cewa shi ne shugaban kungiyar, ya fito cikin wani faifan bidiyo a wannan makon yana daukar alhakin hare-haren da aka kai a garuruwan Baga da Bama, har ma yana cewa kungiyar zata fara satar jama'a tana garkuwa da su a wani bangaren cimma muradunta.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun soki lamirin gwamnatin Najeriya saboda yin amfani da karfi fiye da kima tare da kashe fararen hula a kokarinta na kawo karshen tashin hankalin Boko Haram.

Mutanen garin Baga sun ce dakarun tsaro sun kona dubban gidaje a garin a bayan da 'yan Boko Haram suka kashe wani soja. Rundunar sojojin Najeriya ta musanta wannan zargin.

Shugaba Goodluck Jonathan ya fada jiya talata cewa za a ba sojojin da za a girka a wadannan jihohi uku ikon kama mutane, da kwace duk wani ginin da ake amfani da shi wajen shirya ayyukan ta'addanci, da kuma tsare duk mutumin da aka samu dauke da makami ba tare da iznin hukuma ba.
XS
SM
MD
LG