Mayan Lauyoyi masu rajin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, na kokawa dangane jan kafa da sashen sharia keyi wajen yanke hukunci a shari’un cin hanci a Najeriya.
Mr. Abraham Onaji, jami’in wata kungiya mai suna” END INPUNITY” dake rajin yaki da cin hanci a Najeriya, yace cin hanci na damun su saboda akwai abubuwa da dama da suka faru har yau ba ayi komai akan su ba, kaga mu a matsayin mu na ‘yan kungiya masu yaki da cin hanci da rashawa mu bama jin dadi idan ka dubi kasashe kamar China, ba’a daukar lokaci idan mutun ya amsa laifinsa ko a daure shi ko kuma kisa.
Wani lauya a Najeriya, Barrister Yakubu Saleh Bawa, ya koka a bisa yadda sashen sharia ke jan kafa a shari’un wawure dukiyar jama’a, yana mai cewa masamman su da suke bangaren sharia dole su kasance cikin damuwa.
Ya kara da cewa idan ma sharia akayi jikirin yin adalci tafkar ma ba’a yi adalcin bane abunda wanna ke haifarwa shine yan haifarwa jama’a shakka da kuma karyamasu karfin guiwa cewa gwamnati da take mulki zata tabbatar da gaskiya da adalci ko da yaushe a hanzarta tabbatar da anyi wadanna shari’un kuma a gama bisa ga lokaci.
Itama kungiyar nan dake rajin yaki da cin hanci a Najeriya, wato “ Progressive Mind For Development Initiative” har takardan koke ta aike ga shugaba Muhammadu Buhari, in ji babban jami’in ta Kwamarade Abubakar Abdulsalam.
Shugaban kwamitin cin hanci da rashawa a Najeriya, Farfesa Osagie, yace abun takaici ne ga tsarin sharia Najeriya, tsari ne daya karye kuma ake kan kadon jinya kuma ake masa Karin jinni amma bai samun sauki. Tsarin shariar mu tsari ne da rubabbun da gurbatattatun manyan Lauyoyi suka yi ragaraga dashi in ji Farfesa Osagie.