Yanzu haka dai Sarakunan gargajiya na wannan yankin sun fara wani shirin farfado da zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da Manoman.
Domin magance wannan matsalar ne yasa yanzu manyan sarakunan jiha masu daraja ta daya tashi tsaye, Kanal Steven Mai Ritaya shine babban sarki a al’umar Bachama, yace abin takaici ne abubuwan da ke faruwa a jihar, inda yace “A kwai jahilci a kasa, wani an kashe masa ‘dan uwa bai san ba yadda zai yi ba sai yaje yace zai rama.” Inda ya ci gaba da cewa ba’a san mutanen Adamawa ba da irin wannan hali ba, domin idan Boko Haram ta saci mutanen jihar to tabbas a san yadda za a yi.
Sarakunan dai sunyi taro kan yadda za a shawo kan bangarorin biyu, inda suka bukaci al’ummar yankin da su rike juna tamkar kowa ‘daya ne, ba tare da nuna bambamcin addini ko na kabila ba.
Sanata Abdul’aziz Nyako ‘dan majalisar dattawa mai wakiltar Adamawa ta tsakiya, inda aka samu irin wannan tashin hankali cikin kwanakin nan. Yace dama can ana samun irin wannan, shakaru uku da suka gabata ma karin rigimar ta faru aka sanar musu inda suka ‘dauki wani matakin sulhu aka shawo kan mutanen.
To sai dai kuma ya zuwa yanzu kuma mutanen da wannan rigima ta shafa na cikin wani mawiyacin hali, shima wani daga cikin shugabannin al’umomin da abin ya shafa Mr. Victor Nashamdam ya bayyana halin da ake cikin, inda yace an kone garuruwa har guda hudu.
Saurari cikakken rahotan Ibrahim Abudul’aziz daga Yola.