Ita dai wannan cutar an dangata ne da haihuwa a kudancin Amurka, hukumar tace wannan cutar tana nema ta zama alakakai ga sauran sassan duniya.
Jiya ne dai hukumar ta dauki wannan matakin, tace duk da yake ba samu wata kwakkwarar hujja ba cewa sauro ne ke haddasa mummunar illa ba ga kwakwalwan jarirai musammam a Brazil bayan da cutar da barke a shekarar 2013-14.
Yanzu haka dai rahotanni sun tabbatar cewa ciwon kwakwalwa wanda ke karuwa cikin jarirai wadanda suka kamu da cutar sai kara bazuwa yake yi a sassan da wannan cutar ta barke.