Kakakin wannan tawaga, Malam Ibrahim Mohammed, yace su na son su bayyana adawarsu da yunkurin da Malam Yakubu Dogara, dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tafawa Balewa da Bogoro da Dass, yake yi a majalisar na neman ganin an sake maido da hedkwatar karamar hukumarsu zuwa garin Tafawa Balewa.
Kwanakin baya ne majalisar dokokin Jihar Bauchi, ta yi dokar da ta dage hedkwatar karamar hukumar daga garin Tafawa Balewa zuwa garin Bununu, a wani mataki na kawo karshen fadan da ya ki ci ya ki cinyewa da aka yi ta gwabzawa na kabilanci da addini a garin Tafawa Balewa.
Ga rahoton Abdulwahab Mohammed daga Bauchi kan yadda wannan batu ya kaya a harabar majalisar.