Jihar dai tana faman da kokarin murmurewa daga rikicin addini da na kabilanci da ya auku a Wukari. Shugabannin sun kira 'yan siyasa ne domin kada su sake jefa jihar cikin wani rikicin. Garkuwan Jan Alhaji Abubakar Dauda wanda ya gina masallaci da mijami'a a garinsu ya ce ya yi mamaki yadda wasu 'yan siyasa ke anfani da addini da kabilanci su haddasa rigingimu a jihar. Ya ce duk wanda ya ce an cuceshi sabili da addini ko kabilanci karya yake yi, Shi ma Marcus Hamidu mai rike da makamai da dama cewa ya yi Musulmai da Krista su shiga masallatai da mijam'u su fada wa mutane gaskiya.
Jihar Taraba jiha ce da ta kunshi kabilu daban-daban da addinin Islama da da Krista. Gwamnan jihar Alhaji Umar ya ce kokarinsu kullum shi ne su tabbatar da zaman lafiya domin a cikin jihar kusan kowane iyali na da Musulmai da Krista a cikinsa. Don haka dole ne a nemi zaman lafiya da juna idan a na son cigaba.
Abdulwahab Mohammed nada karin bayani.