Jagoran kungiyar Mr. Ezekiel Gomos ya bayyana dalilin shiya taron. Ya ce sun shirya taron domin inganta zumunci, su fada ma juna gaskiya, su kuma gafartawa juna domin a koma yadda ake da can. Ya ce idan ba'a zauna tare ba to ba za'a san abubuwan dake damun kowane bangare ba. Zasu cigaba da yin irin wannan taron a lokuta daban daban da ma bita.
Musulman da suka halarci taron shan ruwan sun yaba da kokarin kuma sun yi farin ciki. Sun bada tabbacin hadin kai domin samun zaman lafiya da aka yi yanzu ya dore. Shugaban kungiyar Krista reshen Jos Ta Arewa shi ma ya ce ya yi murna kuma ya dauki alkawarin tara duk fastoci ya fadakar da su domin cigaban zaman lafiya. Da yake mayarda martani Kwamishanan Labarai na Jihar Pilato Abraham Yiljap cewa ya yi harakar tsaro ko zaman lafiya ba na mutum daya ba ne. Abun da kungiyar ta yi abun koyi ne ga kowa. Shi ma kwamandan rudunar soji ya ce akwai wadanda basa son zaman lafiya domin suna kudi da rikicin. Don haka ya kira mutane da su guje ma masu son tada zaune tsaye.
Zainab Babaji nada rahoto.