Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

“Na Dauki Kaina Mai Sa'a”: Wani Mutumin Da Ya Haye Gadar Baltimore Jim Kadan Kafin Rugujewarta


Gadar Francis Scott Key, Maryland da ta ruguje
Gadar Francis Scott Key, Maryland da ta ruguje

Da misalin karfe 1 na safe ranar 26 ga Maris ne Larry DeSantis ya nufi aikinsa na biyu a gidan burodin Herman da ke yankin Baltimore.

WASHINGTON, D. C. - A lokacin ne dai wani jirgin ruwa ya yi karo da gadar Francis Scott Key, wanda ya haifar da rugujewar gadar inda a ya kai ga tsallake rijiya da baya.

Gadar Maryland
Gadar Maryland

DeSantis ya ce ya yi imanin cewa yana daya daga cikin mutane na karshe da suka sauka daga kan gadar kafin wannan mummunan hadarin. A cikin wata hira da gidan talabijin na CNN, ya tuna da cewa motarsa ta haye, "ya kuma mai da hankali kan mutanen da ke kan gada" da kuma ƙoƙarin tuƙi a hankali a kusa da su.

“A gaskiya ban ma ga jirgin ko kadan ba. Na dai maida hankali ne kawai kan abin da ke gabana.”

Alamar kawai wani abu ba daidai ba shine abin da DeSantis ya bayyana a matsayin rashin ababen hawa, har da sanyin safiyar.

"Akwai wata motar a bayana," in ji shi. "Tarakta ce, amma ba ta da tirela saboda haka sai na shiga gabansa daidai lokacin da muka fara haye gadar."

Bidiyon kyamara mintuna biyar na ƙarshe kafin karon ya nuna motar da za ta iya dacewa da ta DeSantis a lokacin da kuma motar tirela da ke biye, kodayake bidiyon bashi da haske sosai.

Motoci shida ne kawai suka bi ta wannan layin kafin jirgin ruwan mai tsawon ƙafa 984 ya bugi ɗaya daga cikin ginshiƙan gadar da ƙarfe 1:29 na safe a cewar jaridar Baltimore Banner da ta fara ba da labarin DeSantis.

Rugujewar ta jefa motoci da mutane cikin kogin Patapsco mai tsananin sanyi. Ma’aikata shida da suke gyaran ramuka a kan gadar an ba da rahoton bacewarsu a sakamakon haka; Yanzu haka dai an gano gawarwakin biyu a cikinsu. Sauran hudun kuma ana kyautata zaton sun mutu.

"Idan da na tsaya na yi magana da wani, abokin aikina a kan gadar koda na minti daya, da alama da ba zan kasance a nan ba a yau," in ji DeSantis.

Mintuna bayan wucewar DeSantis kan gadar, daya wurin aiki na sa suka kira don duba shi.

"Wani ya kira ni kamar bayan misalin mintuna biyu ya ce, 'A ina kake?' Shi ne daga daya wurin aikin nawa," in ji shi. "Na ce yanzu kawai na haye gada, sai suka ce, 'To kana sane cewa yanzu gadar ta ruguje."

DeSantis ya ce ya kasa yarda da abin da aka gaya mishi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG