Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawarwakin Ma'aikata 2 Daga Cikin Shida Da Suka Nutse Cikin Kogin Baltimore Da Ke Jihar Maryland


Maryland Bridge Collapse
Maryland Bridge Collapse

Jiya Laraba, masu bincike sun fara tattara abubuwan kafa shaida daga cikin jirgin ruwan da ya hankade wani sashin gadar Francis Scott a ranar Talata.

An gano gawarwakin ma’aikata biyu da safe cikin wata jar motar daukar kaya wace ta nitse cikin ruwa da akalla zurfin mita 7.6 kusa da tsakiyar gadar, kamar yadda kanar Roland L. Butler Jr., shugaban hukumar ‘yan sandan jahar Maryland ya gaya wa manema labarai a wurin wani taron manema labarai da yammacin jiya.

Sai da aka tabbatar da lafiyar jirgin dakon kayan da ya yi hatsarin kafin ya dauke wuta aka kasa sarrafa shi har ya daki wani sashin wata gada a Baltimore a tashar, a binda masu tsaron teku a Amurka suka fada jiya Laraba kenan, yayin da masunta suka gano gawarwakin mutum 2 daga cikin ma’aikata 6 da suka fada cikin ruwan a sa’adda gadar ta rufta.

Ana kyautata zaton cewa sauran mutanen sun mutu sannan jami’ai sun ce an yi iya neman da za iya.

Ya ayyana mutanen da Alejandro Hernandez Fuentes mai shekaru 35 wanda ya kasance dan kasar Mexico mazaunin Baltimore da kuma Dorlian Ronial Castillo Cabrera, mai shekaru 26, dan kasar Guatemala mazaunin Dundalk a Maryland.

Mutanen da lamarin ya rutsa da su, sun kasance cikin ma’aikatan da suke gyaran hanya akan gadar kuma su asalin ‘yan kasashen Mexico, Gautemala, Honduras da El-Salvador ne, a cewar Butler.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG