Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane bakwai sakamakon wata girgizar kasa mai karfin maki 6.7 da ta afku a tsibirin arewacin Hokkaido dake Japan.
Hukumar hasashen yanayi ta Japan ta ce an gano gabar girgizar kasar da tayi zurfin Kilomita 40 a gabas da birnin Tomakomai. Bala'in ya haifar da zaftarewar kasa da ta binne daruruwan gidaje da kuma kwararar tabo a kan hanyoyin kauyukan wurin.
Wutar lantarki ta dauke a kusan duka gidaje kimanin miliyan 3 da ke tsibirin. Haka kuma an rufe hanyoyin jiragen kasa na tsibirin gami da sabon filin jirgin sama na Chitose.
Kafar yada labarai ta NHK tace mutane 140 ne suka ji rauni ana kuma zaton kimanin mutane 40 ne suka bata a yayin da masifar ta afku.
Facebook Forum