Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar A Dauki Matakin Kare Yaran Ukraine Daga Rasha - Amurka


UKRAINE-CRISIS/CHILDREN-RETURN
UKRAINE-CRISIS/CHILDREN-RETURN

Akwai bukatar kare 'yan gudun hijirar Ukraine, musamman wadanda suka fi rauni, kamar yara. "Babu tantama yakin da Rasha ke yi a Ukraine ya yi tasiri sosai a kan yaran Ukraine," a cewar Beth Van Schaack, jakadiyar Amurka a ofishin sa ido kan manyan Laifuka a Duniya a ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

A kwanan nan babban sakatare janar din Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da rahotonsa na shekara-shekara kan yara da tashin hankalin makamai, wanda ya gano "laifukan cin zarafin yara guda shida," a cewar jakadiya Van Schaack.

“Rahoton ya tabbatar da cewa a shekara ta 2022 kadai, sojojin Rasha da kungiyoyin da ke da alaka da su ke da alhakin kisa da raunata daruruwan yara, aikata fyade da cin zarafin yara ‘yan mata, da kai daruruwan hare-hare a makarantu da asibitoci, sace yara, sannan da amfani da makarantu da asibitoci don ayyukan soja, da kuma hana kai agajin jinkai.”

Hakika, sojojin Rasha sun sha raba yaran Ukraine da iyayensu a kan dole, bayan haka sun kai su Rasha.

“Wani rahoton kungiyar sa ido kan rikice-rikice da Amurka ke daukar nauyinsa ya ba da cikakken bayani kan tarin shafukan yanar gizo na Rasha da tsare-tsaren ayyukan tura dubban yaran Ukraine wasu yankuna da ke karkashin ikon gwamnatin Rasha, a cikin Ukraine da kuma cikin Rasha, ana kuma gabatar da su a shirye-shiryen sauya tunani a fannin siyasa da kuma duk abinda ya shafi Rasha. Mun san cewa daga duk wandannan bincike-binciken jami'ai a kowane mataki na gwamnatin Rasha suna da hannu, daga Shugaba Putin da kansa, har zuwa jami'an kananan hukumomi wadanda ke taimakawa wajen wadannan ayyuka.

Amurka na aiki tukuru domin magance matsalar cin zarafin yaran Ukraine. A misali, ofishin sa ido kan manyan laifuka a duniya yana goyon bayan kungiyar Atrocity Crimes Advisory, "wani shiri da Amurka, Birtaniya, da Tarayyar Turai suka fito da shi don sama wa ofishin Babban mai gabatar da kara na Ukraine da sauran hukumomin da ke sa ido kan laifukan yaki a Ukraine taimako a kokarin da suke yi a kotunan kasar," a cewar jakadiya Van Schaack. Kungiyar "ta kawo kwararru a fannoni dabam daban kuma daga kasashe da yawa don taimakawa wajen karba da ajiye hujjoji, da kuma binciken manyan laifuka a kasa da kasa.”

“Sauran sassan ma’aikatar harkokin waje na aiki tare da abokan huldarmu da kuma mambobin kungiyoyin farar hula don sauya tare da hana gwamnatin Rasha tisa keyar yaran Ukraine zuwa Rasha, Belarus, da kuma wasu sassan Ukraine da Rasha ta mamaye a kan tilas. Kuma muna sanya takunkumi a kan mutanen da za a iya ganowa da suke da hannu a wannan babban tsari na sace yara.”

"Mun fahimci cewa akwai babban aiki a gabanmu na tabbatar da an hukunta wadannan laifukan kuma zai bukaci kokarin dukkan bangarorin gwamnatin Amurka. "Mun kuduri aniyar cimma wannan burin."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG