Jami’an kasar Italiya sun ce akalla mutane 70 sun bace wasu mutane uku kuma sun mutu, yayinda wani jirgin ruwa na ‘yan yawon bude ido yayi hadari ba nisa da gabar ruwan Tuscany dake cikin kasar a daren jiya Jumma’a.
Wan nan adadi na wadan da suka halaka bai kai yawan abinda aka bada rahoton sun halaka tunda farko ba.
Hukumomi suka ce jirign mai suna Costa Concodia, wanda yake dauke fasinjoji da ma’aikatan jirgi sama da dubu hudu ya samu matsala ne kusa da tsibirin Giglio. Fasinjoji suna shirin cinabincin dare lokacinda lamarin ya auku.
Wata fasinja ta gayawa wata kafar yada labaran Italiya cewa mutane sun rude, kamar yadda take cewa “ tamkar abinda ya faru cikin jirgin ruwan nan na Titanic, wadda yayi kaurin suna da ya nutse a 1913.
An bada rahoton wasu fasunjoji sun yi tsalle suka fada cikin ruwan kankara domin gudu daga jirgin da ya tsage ruwa ya fara kwasan ruwa.
Jami’ai suka ce an ceci fasinjojin ta wajen amfani da kananan jiragen aikin ceto da kuma jiragen sama masu saukar ungulu aka kwashe su zuwa tsibirin Giglio da kuma da kuma Porto Santo Stefano.
Jirgin mai tsawon meta metan da 90 yana da bene 13, mashaya biyar, wuraren cin abinci 4, wureren ninkaya hudu, da kuma manyan dakunan kwana masu varanda dari biyar.
Ana ci gaba da binciken musabbabin wan nan hadari.