Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Bagadaza, Mutum 53 Sun Mutu.


Jami'an tsaro da mutane suke duba wurinda aka kai harin kunarbakin wake a Basra.
Jami'an tsaro da mutane suke duba wurinda aka kai harin kunarbakin wake a Basra.

An kai wani harin kunar bakin wake a Bagadaza, ya halaka akalla mutane 53. Hukumomin kasar suka ce harin da aka kai yau Asabar an auna shi ne kan tawagar masu aikin ibadar ‘yan shi’a kusa da birnin Basra.

An kai wani harin kunar bakin wake a Bagadaza, ya halaka akalla mutane 53.

Hukumomin kasar suka ce harin da aka kai yau Asabar an auna shi ne kan tawagar masu aikin ibadar ‘yan shi’a kusa da birnin Basra. Harin ya raunata akalla wasu mutane 100. Fashewar ta auku ne kusa da wani wurin duba motoci dake kan hanyar zuwa wani masallacin ‘yan shi’a.

An kai harin ne a dai dai lokacinda ‘yan shi’a suke azamar zuwa masallacin domin wasu ayyukan ibda na musamman. An tsananta matakan tsaro sabo da jerin hare hare da ake ta aunawa kan ‘yan shi’a a makonnin baya bayan nan.

Zaman dar dar yayi tsanani tsakanin ‘yan shi’a da 'yan Sunni a Iraqi, musamaman bayan janyewar sojojin Amurka a kasar bara.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG