A farkon makon gobe sakatariyar harakokin wajen Amurka, Hillary Clinton za ta ziyarci wasu kasashe hudu a yammacin Afirka da nufin karfafa muhimmancin yin shugabanci na gari da kuma bunkasar tattalin arziki.
A jiya Jumma’a Ma’aikatar Harakokin wajen ta Amurka ta yi sanarwar rangadin na kwanaki biyu.
Mai magana da yawun ma’aikatar Victoria Nuland ta ce rangadin farkon da Clinton za ta yi a cikin wannan shekara zai kai ta kasar Laberiya domin ta halarci rantsar da shugaba Ellen Johnson-Sirleaf a wa’adin mulkin ta na biyu. Daga Laberiya kuma za ta yada zango a kasashen Ivory Coast da Togo da kuma Cape Verde.
A kasar Ivory Coast za ta gana da shugaba Alassane Ouattara kamar yadda aka shirya.
Victoria Nuland ta ce Clinton ce sakatariyar harakokin wajen Amurkar ta farin farkon da za ta taba kai ziyara kasar Togo. Za ta gana da shugaba Faure Gnassingbe domin ta bayyanawa kasar Togo goyon bayan Amurka saboda ci gaban demokradiyar da ta samu da kuma aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, kuma domin ta taya kasar murnar samun kujerar da ba ta dindindin ba a kwamitin sulhun MDD a wannan shekara da shekara mai zuwa. Amurka na kara neman goyon bayan kasa da kasa domin a kara takurawa Iran da Syria.
Clinton za ta kammala rangadin na ta da kasar Cape Verde, inda za ta gana da Frayim Minista Jose Maria Neves domin tattauna yadda za su hada kai game da wasu batutuwa, kamar su cinikin haramtattun abubuwan sa maye a yankin.