Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 26 Suka Rasa Rayukansu A Wani Fashe-fashe Kusa Da Ofisoshin 'Yan Takara A Pakistan A Jajibirin Zabe


Mutane 26 Suka Rasa Rayukansu A Wani Fashe-fashe Kusa Da Ofisoshin 'Yan Takara A PakistanA Jajibirin Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:36 0:00

Mutane 26 Suka Rasa Rayukansu A Wani Fashe-fashe Kusa Da Ofisoshin 'Yan Takara A PakistanA Jajibirin Zabe

Wasu fashe-fashe guda biyu a kusa da ofisoshin 'yan takara a lardin Balochistan na kudu maso yammacin Pakistan sun kashe mutane 26 tare da jikkata wasu da dama, a cewar jami'an yankin a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu, lamarin da ya kara nuna damuwa kan tsaro a jajibirin babban zabe.

WASHINGTON, D. C. - Pakistan za ta kada kuri'a a ranar Alhamis 8 ga watan Fabrairu; a daidai lokacin da ake samun karuwar hare-haren 'yan bindiga a cikin 'yan watannin nan da kuma tsare Imran Khan, wanda ya lashe zaben kasar da ya gabata, wanda ya mamaye kanun labarai duk da rikicin tattalin arziki da wasu matsaloli da ke barazana ga kasar mai makaman nukiliya.

Pakistan
Pakistan

Hukumomin kasar dai sun ce suna karfafa matakan tsaro a rumfunan zabe. Harin farko wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 14, an kai shi ne a ofishin ‘dan takarar zabe mai zaman kansa a gundumar Pishin.

Pakistan
Pakistan

Fashewar na biyu a garin Qila Saifullah da ke kusa da kan iyaka da Afganistan ya tarwatse ne a kusa da ofishin Jamiat Ulema Islam (JUI), jam'iyyar addini da a baya ta sha kai hare-hare kamar yadda ministan yada labaran lardin ya bayyana.

Pakistan
Pakistan

PAKISTAN
PAKISTAN

Mataimakin kwamishinan Qila Saifullah, Yasir Bazai ya ce mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar bam din da ta samo asali daga wani babur da aka ajiye a kusa da ofishin, sannan 25 suka jikkata.

Kawo yanzu dai ba a bayyana ko su waye suka kai hare-haren ba.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG