Binciken da aka yi ya nuna cewa an dan samu tashin farashen kaya. Duk da cewa kusan kashi saba'in da biyar na masu sayar da kaya Musulmai ne amma abun mamaki shi ne basa jin tausayin 'yanuwansu Musulmai kamar yadda wani malam Yahaya Sambo ya fada. Ya ce basu da tausayi ko imani. Sai Malam Musa Auna shugaban cibiyar kasuwanci a jihar Neja ya ce suna kokarin jawo hankalin 'yan kasuwa da su rage farashan kayansu. Ya ce zasu jawo hanakalin 'yanuwa 'yankasuwa da su duba idan lokacin Kirsimati ya yi 'yankasuwa kiristoci suna yi ma kirista ragowa. Yayi mamaki yadda Musulmai ba zasu yin koyi da wannan ba.
To a wata sabuwa kuma Alhaji Sadiq Mohammed Wudil wani babban dan kasuwa a kasuwar Gwari cewa ya yi ba'a samu karin farashe ba kuma kafin a kama azumi zasu kara sauka.
Kodayake babu wani abun da gwamnati ta ce talakwa na fatan gwamnati zata taimaka da hatsi kamar yadda a ke yi a can baya.