Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maniyantan Jihar Adamawa Sun Shiga Fargaba sanadiyar rage kujerun zuwa hajji da gwamnatin Saudiya ta yi a wannan shekarar


Maniyanta a kasa mai tsarki
Maniyanta a kasa mai tsarki

Maniyanta a kasa mai tsarki suna aikin ibada

Maniyantan Jihar Adamawa sun shiga fargaba sanadiyar rage kujerun zuwa hajji da gwamnatin Saudiya ta yi a wannan shekarar domin wani gagarumin aikin fadada wuraren ibada a kasa mai tsarki.

A ta bakin wasu da suka damu ainun sun ce dama can a shekarun da suka wuce ba duka mutane da suka biya kudin tafiya ke samun yin tafiyar ba ta dalilin kayyade kujerun da ake ba kowace jiha. Yanzu kuma da gwamnatin Saudiya ta rage kujerun a jihar Adamawa akalla mutane dari hudu ne ba zasu samu tafiya ba.

Jami'an hukumar aikin hajji a jihar sun ce ba zasu bari duk wadanda suka je hajji da ba dama su sake zuwa a wannan lokacin. Ma'ana, dole ne su bar wadanda basu taba zuwa ba zarafi. Duk da haka ba duka wadanda basu taba zuwa ba zasu ci nasarar zuwa. Inji ta bakin wani jami'i sun kasa mutane kashi uku. Akwai wadanda suka fara biya tun can farko. Akwai wadanda suka biya a tsakiyar shirin. Akwai kuma wadanda suka biya daga baya.

A cewar jami'in wadanda suka fara biya za'a ba fifiko daga bisani sai ayi cacar tafiya. Wanda ya dauki takarda da tace Saudiya ya ci ke nan. Wadanda suka dauki takarda da tace Najeriya sai ya hakura. Amma ya yi alkawarin cewa duk wadanda basu samu tafiya ba a wannan karon su ne kan gaba a shekara mai zuwa.

Wakilin Muryar Amurka nada karin bayani.


please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG