Mataimakin shugaban sadarwa na kungiyar Alhaji Nasir ya yiwa wakiliyarmu karin bayani kan abubuwan da suka tattauna a taron.Ya ce kungiyar ta lura da irin matsalar tsaro da kasar ke ciki dalili ke nan da suka sa ma taron taken Tsaro a Mahangar Musulunci da kuma yin Adalci a Bangaren Shugabanni. Ya ce tun da za'a shiga watan ramadan ya kamata su ba rassansu na kasa da kuma waje wani guzuri na musamman. Don haka mun yi kokari mu karantar da su tauhidin kadaita Allah, samun kyakyawar tarbiya da mahimmancin abun da ya shafi fadar gaskiya da rikon amana da kuma tsayuwa a kan yaya tsaro zai kyautatu, in ji Alhaji Nasir.
Da aka tambayeshi wacce gudummawa kungiyar ke bayarwa wajen hadin kai da inganta tsaro sai ya ce "a cewa mutane su zauna lafiya su kuma yi addini babbar gudunmawa ce". Ya kara da cewa samun kungiyar a Najeriya ta ce a bari a kuma barin ai shi ma gudunmawa ne." Amma babbar gudunmarwar ita ce kada a yi abu mara kyau. Mai shan giya ya bari. Mai zina ya bari. Mai caca ya bari.Idan mutane suka daina yin laifi ai an kawo gudunmawa".
Dr. Nuhu Tahir Tajudeen shi ne shugaban sadarwar kungiyar a Jihar Kaduna. Ya ce muhimmin abun da aka koyar a taron shi ne da'a ga Allah Tabaraka Wata ala da da'a ga magabata wadanda Allah Ya ce ayi masu da'a. Abu na biyu shi ne hadin kai. Duk abun da za'a yi a hada kai a yi domin haka Allah Ya yi umurnin a yi. Ya ce matuka
kowa ya ci tsoron Allah ba za'a samu matsala ba. Ya ce duk abubuwan da suke faruwa aiki ne na shaidan da rashin tsoron Allah.
Wasu da suka halarci taron sun ce sun karu da fahimta musamman game da watan ramadan dake karatowa da albarkarsa da kuma kokarin da yakamat su yi domin su samu albarkan watan.
Zainab Babaji nada karin bayani.