Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MURIC Ta Bayyana Damuwa Game Da Zargin Shirin Tube Sarkin Musulmi


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Babban daraktan kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana damuwar a cikin sanarwar daya fitar a yau Litinin, inda yace al'ummar Musulmin Najeriya ba zasu amince da duk wani tunani na tube Sarkin Musulmi ba.

Kungiyar kare hakkin Musulmin Najeriya (MURIC) ta bayyana damuwa game da zargin cewar gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu na shirin tube Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Babban daraktan kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana damuwar a cikin sanarwar daya fitar a yau Litinin.

A cikin sanarwar, Farfesa Akintola yace al'ummar Musulmin Najeriya ba zasu amince da duk wani tunani na tube Sarkin Musulmi ba.

Rade-radin dake yawo na nuni da cewar gwamnan na dira kan Sarkin Musulmin a kowane lokaci daga yanzu ta hanyar bada uzurin da yayi amfani dashi wajen cire sarakunan gargajiya 15 da yayi a baya.

"MURIC ta baiwa gwamnan shawarar cewar ya duba kafin ya sara. Kujerar Sarkin Musulmi ta zarta ta al'ada. Kujera ce ta addini. Kuma hurumin sarkin ya zarta iya kasar Sokoto. Hurumi ne daya karade fadin Najeriya. Shine jagoran addinin ilahirin Musulmin kasar."

Don haka duk gwamnan daya kuskura ya taba alfarmar kujerar Sarkin Musulmi, toh, gashi nan ga Musulmin Najeriya saboda bayan mukamin Sarkin Musulmi kuma shine Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, a cewar Akintola.

Shugaban kungiyar ta MURIC ya yi gargadin kada Gwamna Ahmad Aliyu ya jawowa kansa fushin al'ummar Musulmin Najeriya.

"Domin kauda shakku, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ba wai kawai Sarkin Musulmin Sokoto bane, a'a shine sarkin al'ummar Musulmin Najeriya. Nasarori daya samu da salon jagorancinsa sun sa ya shiga zukatan al'ummar Najeriya"

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin al'amura da cece-kuce ke kara kamari game da raba wasu sarakuna da kujerunsa da aka yi a jihar Kano.

A baya gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu ya sauke wasu sarakuna 15 daga kan kujerunsu akan dalilai daban-daban.

Har yanzu gwamnatin jihar Sokoto bata ce komai ba game da zargin na kungiyar MURIC, saidai a baya tace akwai shirye-shiryen yin gyara akan sashe na 79 na dokar kananan hukumomi da harkokin masarautun jihar domin tayi daidai da al'adun jihar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG