Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Badakalar Biliyan 165: PDP Ta Bukaci A Cire Ministan Sufuri Rotimi Amaechi


PDP, Shugaba Muhammadu Buhari
PDP, Shugaba Muhammadu Buhari

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bukaci da a gaggauta cire Ministan sufuri na kasar Rotimi Amaechi, sakamakon zarge-zargen sama da fadi da naira biliyan 165 na hukumar tashoshin ruwan kasar.

Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar ta PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar, ta yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya sa a gudanar da cikakken bincike da kuma gurfanar da Ministan na sufuri a gaban kuliya, tare da tsohuwar babbar daraktar hukumar tashoshin ruwan kasar Hadiza Bala Usman, dangane da zargin sama da fadi da kudade fiye da naira biliyan 165 na hukumar.

A makon jiya ne shugaba Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman daga mukaminta, biyo bayan shawarar da Amaechi ya bayar, kan cewa rahoton binciken kudade ya nuna cewa hukumar ta tashoshin ruwan kasar, ta ki ta sanya kudaden shiga naira biliyan 165 a Baitul malin kasar.

Hajia Hadiza bala Usman
Hajia Hadiza bala Usman

Bayan dakatar da babbar daraktar, Ministan ya kuma kafa wani kwamitin bincike mai wakilai 10, domin binciken ayukan tara kudin hukumar daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

To sai dai jam’iyyar ta PDP ta kalubalanci salon Ministan na kafa kwamitin da ya kumshi jami’an ma’aikatarsa domin bincikar lamarin.

Karin bayani akan: Hadiza Bala Usman, Rotimi Amaechi, EFCC, PDP, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A cewar PDP, kamata yayi su duka biyun, wato minista Amaechi da Hadiza Bala Usman, duk a mika su ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, domin ta binciki lamarin da kuma hukunta su.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa akwai wata makarkashiya da Ministan ke son rufewa, “dalili ke nan da ya sa Ministan bai tashi binciken babbar daraktar ba shekaru 6 da suka gabata da yayi aiki da ita, sai a yanzu.”

Rotimi Amaechi, Ministan Sufurin Najeriya
Rotimi Amaechi, Ministan Sufurin Najeriya

Tuni dai da babbar daraktar Hadiza Bala Usman ta fito kara ta musanta zargin na Rotimi Amaechi, inda a cikin wata wasika da ta aikewa fadar shugaban kasa da saura wurare, ta bayyana cewa akwai kuskure a kididdigar kasafin kudin hukumar da na kudaden shigar da take tarawa.

Haka kuma ta nisanta kan ta da aikata ba daidai ba da kudaden shigar hukumar har naira biliyan 165, kamar yadda Ministan yayi korafi.

Wannan lamari kuma ya janyo ra’ayoyi mabambanta a tsakanin masu lura da al’amura a Najeriya.

Wasu na kallon lamarin ne a zaman bita-da-kulli kawai da Ministan ke yi don ganin bayan babbar daraktar, sakamakon rashin jituwa da ta dade da bayyana a tsakaninsu, duk kuwa da cewa hukumar ta tashoshin ruwa na karkashin ma’aikatar sufuri ne.

Wasu kuma na ganin cewa kamata yayi a gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamari game da kudaden shigar hukumar, musamman saboda yadda masu rike da mukamai a kasar suka yi kaurin suna wajen handame dukiyar kasa.

To sai dai ko baya ga jam’iyyar ta PDP, masu fashin baki da dama na bayyana ra’ayin cewa ba irin kwamitin da Ministan ya kafa ne ya kamata ya binciki lamarin ba, saboda fargabar rashin adalci kan iya shigowa, kasancewar membobin kwamitin akasari ma’aikata ne da ke karkashin Ministan.

XS
SM
MD
LG