A cikin wata wasika zuwa ga shugaban hukumar ta EFCC Abdulrasheed Bawa, da babban dogarin Sufeto Janar, Idowu Owohunwa ya sanya wa hannu a madadin mai gidansa, ta bukaci da a gaggauta sakin dukkan manyan jami’an ‘yan sanda, daga mukamin babban sufuritanda (CSP) zuwa sama da aka tura a hukumar.
Wasikar mai lamba 3380/IGP.SEC/ABJ/VOL.3/547, ta kuma umarci jami’an ‘yan sandan da lamarin ya shafa, da su koma ga Owohunwa ya zuwa karfe 10 na safiyar jiya Laraba domin jin mataki na gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa umarnin na Sufeto Janar na ‘yan sanda ya shafi jami’ai 25 masu mukanin CSP kadai da ke rike da muhimman ayuka a hukumar ta EFCC, wanda kuma hakan kan iya shafuwar ayukan hukumar.
Karin bayani akan: Usman Alkali, EFCC, Abdulrasheed Bawa, PREMIUM TIMES, Nigeria, da Najeriya.
Masu lura dan al’amura na siffanta wannan umarnin da ya zo a ba zata, a matsayin wata alama ta zaman doya-da-manja da kan iya kunno kai tsakanin hukumomin tsaron biyu, da ke da tarihin aikin hadin gwiwa, wanda ya taimakawa hukumar EFCC wajen samun ma’aikatan da take bukata domin aiwatar da ayukanta.
To sai dai wasikar ta Sufeto Janar na ‘yan sanda, ta bayyana cewa an dauki matakin ne “sakamakon wata bukatar gaggawa ta aiki da ta taso.”
Haka kuma shugaban ‘yan sandan ya bukaci shugaban EFCC da ya samar masa da jerin sunayen dukkan ‘yan sandan da ke aiki a hukumar, tare da bayyana ranar da aka tura su, da kuma matsayin aikinsu a hukumar.
Duk wannan na zuwa ne watanni 2 bayan soma aikin Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar ta yaki cin hanci da rashawa, haka kuma kimanin sati 2 da nadin Usman Alkali a matsayin mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sanda.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa wasikar ta Sufeto Janar na ‘yan sandan ta zo wa hukumar ta EFCC a ba zata.
Wani babban jami’in hukumar ta EFCC da ya bukaci a sakaya sunansa saboda rashin iznin magana da ‘yan jarida, ya fadawa PREMIUM TIMES cewa, lamarin ya gigiza hukumar matuka, musamman saboda ya zo a daidai lokacin da ba ta ma soma amfana da makudan kudaden da ta kashe wajen horar da jami’an ba.
“Jami’ai ne da ke rike da muhimman mukamai a EFCC. Su ne shugabannin sassan hukumar, a yayin da jami’an bincike da dama ke koyon aiki a karkashinsu. Wasun su ma yanzu haka suna kula da muhimman ayukan kasa a madadin hukumar. Kai! Wannan lamari zai haifar da babban gibi a hukumar," in ji jami'in.
Jami’an ‘yan sanda sun kasance tamkar muhimman gimshikai ga hukumar ta EFCC tun kafa ta a shekarar 2003, a yayin da dukkan shugabannin ta da suka gabata suke da tarihin aikin ‘yan sanda.
Sabon shugabanta na yanzu Abdulrasheed Bawa, shi ne shugaba na farko da aka yi daga jami’an da aka horar daga hukumar da basu taba aikin dan sanda ba.