Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kai Hari a Maiduguri


Wani hari da aka kai a Maiduguri a kwanakin baya
Wani hari da aka kai a Maiduguri a kwanakin baya

An kai wani sabon hari a Maiduguri, babban birnin jahar Borno, inda mutane da dama suka jikkata. Wannan shi ne hari na uku da ya auku a tsakanin kwana guda da yini daya.

Wani harin kunar bakin wake da aka kai a birnin Maiduguri da ke jahar Borno a arewacin Najeriya ya jikkata mutane da dama.

Rahotannin sun ce bam din ya tashi ne a masallaci yayin da ake gudanar da sallar la’asar. Sa dai babu cikakken bayani kan adadin mutanen da suka jikkata.

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce ana can ana baiwa wadanda lamarin ya rutsa da su kulawa.

Babu dai wanda ya dauki nauyin kai wannan hari amma a baya akan dora alhakin hakan akan kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a jahar.

Ko a jiya Juma’a wani hari da kungiyar ta kai a Maiduguri, sai dai ya zuwa yanzu, hukumomi ba su ce uffan ba.

Jami’an tsaro da wadanda suka shaida harin na jiya, sun ce sun harba gurneti ne akan wani gida da ke Maiduguri a daren jiya Juma’a, lamarin da har ila yau ya raunata mutane 17.

Wani mazaunin garin na Maiduguri, ya ce ya ji fashewar abubuwa har sau 40, kafin daga baya kidayar ta bace masa.

Rahotanni sun ce, jim kadan bayan hare-haren, matasa ‘yan banga, sun dauki makamai suka bazama kan tituna domin hana ‘yan kungiyar ta Boko Haram kutsa kai cikin garin.

Wannan hari, ya faru ne kasa da sa’oi 24 bayan da a kai wani hari a wajen wani bikin aure a kauyen Tashar Alade da ke da tazarar kilomita 270 daga birnin na Maiduguri.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce yayin da ake kokarin ceto wadanda bam din farko ya rutsa da su ne wani bam na biyu ya tashi, lamarin da ya hallaka mutane bakwai, ya kuma raunata wasu da dama.

Bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari, ya ce zai mayar da rundunar tsaron kasar zuwa Maiduguri a wani mataki na kokarin dakile shawo kan wannan rikici.

Ga karin bayani a rahoton wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda daga Maiduguri:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG