Wadanda suka shaidalamarin sun ce harin ya faru ne da misalign karfe shida na safe a wani wuri da ake kira Tashan Alade a jahar Borno a lokacin da dangin amarya suka taru domin gudanar da shagulgulan bikin.
Wannan ba shi ne karon farko da aka kai hari a wannan anguwa mba, a baya an zargi kungiyar Boko Haram da kai hare-hare, sai dai yanzu babu tabbacin ko kungiyar ta Boko Haram ce ta kai wannan hari.
Wata mata da lamarin ya auku a unguwarsu ta gayawa Muryar Amurka cewa an kama daya daga cikin maharani kuma jami’an tsaro na gudanar da bincike.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce sun ga lokacin da aka kwashe gawawwakin mutane bakwai a inda aka kai harin, sannan sun ce wasu gidaje guda biyu sun kone.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar da harin sai dai ba ta yi karin bayani kan lamarin ba.
Wannan hari ya faru ne yayin da Najeriya ke bukuwan mika mulki bayan zabukan da aka gudanar a farkon shekarar nan.