Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Fada Ya Sake Barkewa A Juba Babban Birnin Sudan ta Kudu


Shugabannin Sudan ta Kudu
Shugabannin Sudan ta Kudu

Mummunan fada ya barke a yau Litinin a Juba babban birnin Sudan ta Kudu, sa’oi kadan bayan da kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, ya yi kira ga shugabannin kasar da su janye dakarunsu da ke arangama da juna, tare da yin gargadin cewar ci gaba da kai hare-hare akan fararen hula da ma’aikatun MDD ka iya zama laifukan yaki.

Harbe-harben bindiga da fashe-fashe sun yi ta tashi a Juba a yau Litinin, a rana ta biyar bayan da aka samu tsagaitawar al’amura.

Jakadan Kasar Japan, Koro Bessho, wanda shi ne shugaban kwamitin sulhun mai dauke da mambobi 15, ya yi magana da yawun kwamitin a jiya Lahadi a birnin New York, bayan da aka yi wani dogon taron gaggawa na sa’oi ukku na tuntubar juna.

Hayaki ya tashi sanadiyar fadan da ya barke a Juba
Hayaki ya tashi sanadiyar fadan da ya barke a Juba

Bessho ya kwatanta halin da ake ciki a Juban a matsayin wanda ke bukatar sulhu cikin gaggawa, inda ya bayyana cewa har an kashe wani sojan wanzar da zaman lafiya dan asalin kasar Sin tare da raunata wasu ‘yan kasar Rwanda da dama.

Ya zuwa jiya Lahadi hukumomi ba su bayyana takaimaiman adadin mutanen da suka jikkata daga barkewar wannan rikici ba, kuma babu wata alama da ta nuna cewa dakarun shugaba Salva Kiir da na mataimakinsa Riek Machar sun ji wannan kira na Majalisar Dinkin Duniya.

Amma kafofin yada labarai a birnin na Juba sun bayyana cewa an kashe akalla mutane 276, yayin da kakakin Machar ke cewa akalla mutane 150 aka kashe tare da jikkata wasu da dama.

Tuni dai Amurka ta umurci dukkanin ma’aikatanta da ba a bukatar aikinsu cikin gaggawa da su fice daga ofishin jakadancinta da ke Juba.

XS
SM
MD
LG