Kamfanin sadarwa na mtn ya rufe ofisoshinsa dake fadin najeriya.
Sai dai, kamfanin na MTN, ya umarci abokan huldar tasa da suyi amfani da “kafofinsa na intanet” domin samun taimako.
Duk da cewa kamfanin bai bayyana dalilansa na rufewa ba, amma matakin na zuwa kasa da sa’o’i 24 bayan da wadansu fusatattun abokan hukdarsa suka lalata ofishin MTN dake shiyar Festac ta birnin Legas.
Abokan huldar kamfani da aka toshewa layuka saboda sabawa manufar gwamnatin Najeriya ta hada layukan waya da lambar dan kasa sun afkawa ofishin ne domin bayyana korafinsu game da matakin.
Sai dai wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zamunta ya nuna yadda wasu daga cikinsu ke kokarin rusa katangar ofishin.
Hukumomin ‘yan sandan jihar Legas daga bisani suka kai dauki kafin lamura su koma daidai a yankin.
An toshe layukan miliyoyin masu amfani da waya sakamakon gaza hadesu da lambarsu ta dan kasa (NIN).
Matakin dai ya jefa fargaba a zukatan dimbin ‘yan Najeriya.
Dandalin Mu Tattauna