Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Fara Sayar Da Kilo 50 Na Buhun Shinkafa N40, 000 - Minista


Shinkafa
Shinkafa

A cewar Muhammad Idris, matakin na cikin jerin matakan da gwamnatin Shugaba Tinubun ke dauka na saukaka rayuwar ‘yan Najeriya.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci a kwantar da hankula game da zanga-zangar gama-garin da ake shirin yi, inda tace ta kirkiri cibiyoyi a fadin kasar da ‘yan Najeriya zasu je su sayi buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 akan naira dubu 40.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Muhammad Idris ne ya bayyana hakan a jawabinsa ga manema labarai game da batutuwan da aka tattauna a taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jagoranta a fadarsa dake Abuja, a yau Talata.

A cewar Muhammad Idris, matakin na cikin jerin matakan da gwamnatin Shugaba Tinubun ke dauka na saukaka rayuwar ‘yan Najeriya.

Ministan ya kara da cewa babu bukatar gudanar da zanga-zangar gama-garin yanzu tunda Shugaba Tinubu ya fara biyan bukatun masu shiryata.

Ya kuma zayyano shirin baya-bayan nan da gwamnatin tarayyar tayi na rarraba tirelolin hatsi 740 ga jihohin Najeriya, inda yace yanzu za a samu buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 a kan naira dubu 40 a wasu cibiyoyi da aka ware a fadin tarayyar kasar.

“Yanzu za a iya sayen shinkafa akan rabin farashinta, yanzu batun nan da muke ana sayar da buhunan shinkafar. An riga an aika shinkafar zuwa cibiyoyi daban-daban a fadin kasar nan kuma ana sayar da ita ne a kan naira dubu 40. An riga an bude wadannan cibiyoyi domin mutanen dake bukata su je su sayi shinkafar akan naira dubu 40 kowane buhu.”

Ministan ya ci gaba da cewa, gwamnatin tarayya na sa ran farashin kayan abinci ya sauko kasancewa “damina ta kankama.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG