Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Katse Hutu, Ta Kira Zaman Gaggawa


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kira wani taron gaggawa na ‘yan majalisar.

Sanarwar kiran taron, mai dauke da sa hannun akawun Majalisar, Chinedu Akubueze, tace, taron “mai mahimmanci ne ga kasa”.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani game da taron gaggawan ba.

Taron zai gudana ne a ranar Laraba, 31 ga watan Yulin da muke ban kwana da shi, kwana guda kafin fara zanga-zangar gama-garin da ake shiryawa domin adawa da yunwa da tsadar rayuwa.

“Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma, Sanata Godswill Akpabio, ya bada umarnin kiran taron majalisar na gaggawa, a ranar Laraba, 31 ga watan Yulin da muke ciki, da karfe 12 rana”.

“Ana bukatar masu girma sanatoci su yi duk tsare-tsaren da suka kamata domin halartar taron kasancewar za a tattauna batuttuwan da suke da mahimmanci ga kasa. Muna nadamar duk wani rashin jin dadin da katse hutun zai haifar.”

Idan ana iya tunawa majalisar kasa ta fara hutun makonni 7 kuma ana sa ran ta dawo a ranar 17 ga watan Satumba mai zuwa.

An sanar da hutun ne bayan zaman majalisar na Larabar da ta gabata.

Ana sa ran dukkanin zaurukan majalisar guda 2; na Wakilai dana Dattijai su tafi hutu tsawon makonni 7 wanda shine hutunsu na shekara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG