Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai jinkirta wani taron kasashen kungiyar G7 zuwa lokacin ‘fall,” (wato wajejen Satumba da Oktoba). Ya kuma yi kiran da a fadada kungiyar saboda ya na ganin mambobin kungiyar na yanzu sun tsufa sun zama wata tawagar da ba ta wakilci kan abin da ke faruwa a duniya yanzu.
Mambobin kungiyar ta G7 sun hada da Canada da Faransa da Jamus da Italiya, da Japan da Burtanita da kuma Amurka. Trump ya bayyana kasashen Rasha da Australia da Koriya Ta Kudu da kuma Indiya a matsayin wadanda ta yiwu a kara da su.
Da dai Shugabannin kasashe mafiya karfin tattalin arzikin za su gana ne a Amurka wannan shekarar, to amma annobar cutar corona ta kawo cikas ga wannan shirin.
Facebook Forum