Kasashe duniya da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, wato G 7 kamar yadda ake kiransu a dunkule, za su fara taronsu na koli da suke yi shekara-shekara a yau Asabar.
Za a gudanar da taron har zuwa ranar Litinin a wani gari da ake kira Biarritz da ke bakin teku a kasar Faransa, wanda kuma yake da wuraren shakatawa.
Ba wai batun tattalin arziki kadai shugabannin kasashen na G 7 za su tunkara ba, har ma da yadda shugaban Amurka ke yin fito-na-fito da kasashen duniya, musamman da kasashen da suka kasance kawaye na kut-da-kut ga Amurkan.
A lokacin da Shugaba Trump ya ke shirin kama hanyarsa ta zuwa taron a jiya Juma’a, ya yi barazanar saka kudaden haraji akan barasar Faransa da ake shiga da ita Amurka, ko da yake, ya ce, yana fatan zai yi tattaunawa mai muhimmanci da sauran takwarorinsa na duniya.