Kimanin mata dubu daya da dari biyar ne suka halarci taron fadakarwa game da muhimmancin rigafi da kuma zuwa awon ciki ga mata masu juna biyu da gidan rediyon Amurka VOA tare da hukumar kula da kasashe masu tasowa ta Amurka USAID suka shirya a garin Kagara dake jihar Nejan Najeriya.
Shugaban tawagar ma’aikatan muryar Amurka a wannan taro malam Nasiru Yakubu Birnin Yaro yayi Karin haske akan dalilin gudanar da wannan taron fadakarwa ga matan.
Yace, “Gidan radiyon muryar Amurka da hukumar raya kasashe masu tasowa sun saba gudanar da irin wannan taro a jihohi daban daban domin fadakar da masu juna biyu da kananan yara illolin zazzabin cizon sauro da muhimmancin zuwa awon ciki ga masu juna biyu da kuma muhimmancin kai kananan yara rigafi na cututtuka daban daban da ka iya hallaka su.”
Madam Marcy Dawaba, jami’ar yaki da cutar cizon sauro ta ma’aikatar lafiya a jihar Neja ta gabatar da kasida a wurin taron kuma ta yi bayanin cewa duk inda ake gudanar da taro mai muhimmanci irin wannan ya can can ta a kasa kunne domin fahimtar abinda za’a tattauna akai, ta kara da cewa wajibi ne kwararru su tattauna akan yadda za’a kawar da zazzabin cizon sauro.
Shima galadiman Kagara Alhaji Abdullahi Katako yayi bayani akan muhimmancin rigakafin cutar shan inna a wurin taron. Daga karshe mata da dama da suka halarci wannan taro sun yi godiya domin kyaututtukan da suka samu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.