Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Dagawa Aljeriya Kafar Shugabancin Kwamitin Tsaron Afirka


Ginin Ofishin Kungiyar Kasashen Afirka, Addis Ababa
Ginin Ofishin Kungiyar Kasashen Afirka, Addis Ababa

An fara taron kungiyar kasashen Afirka a Kigali babban birnin kasar Rwanda. Sannan maganar zaben kwamitocin kungiyar ne da ta maganar samar da Fasfon tafiye-tafiyen bai daya ga kasashen Afirka ne suka fi mamaye taron.

A baya Najeriya ta so yin takarar shugabantar kwamitin tsaron Kungiyar ta kasashen Afirka, to amma kuma daga baya suka janye. Musamman ganin cewa kasar Algeria da take rike da mukamin tana son tayi tazarce.

Wanda kuma Ministan harkokin wajen Najeriya Mista Jeffrey Onyema yace da za a daga taro to da kila Najeriyar ta tsayar da nata dan takarar, duk da cewa Algeria na son yin tazarce na shugabantar kwamitin tsaron.

Wani kwararren akan harkar diflomasiyya kuma tsohon jakadan Najeriya a kasar Sudan Ambasada Sulaiman Dahiru kwa cewa yayi wannan tunanin shirme ne, inda Najeriya na son tsaida dan takara kawai ta tsayar.

Maganar samar da fasfo na bai daya ga ‘yan kasashen Afirka na daya daga batun da ake tattaunawa a wannan taron da ake a Kigalin, wanda shima wannan batu ne da Ambasada Sulaiman din yace akwai matsala.

Shima mai tsokaci game da harkokin tsaro kuma tsohon jami’in tsaro Aliko Elrasheed Amin yana kallon al’amarin a matsayin wata barazana ga lamuran tsaro a kasashen Afirka in har aka cewa ‘yan kasashen suna da Fasfo din shige da fice kasashen juna na bai daya.

Wakilinmu Hassan Maina Kaina na da cikakken wannan rahoton a cikin makalar sauti ta kasan wannan shafin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG