Wannan kuma damace ta kawar da tunanin matasan daga shiga munanan dabi’u da zaman kashe wando.
Matsalar ayyukan yi a tsakanin matasa na daga cikin manyan abubuwan da ke sa matsa su baude a Najeriya, inda sukan shiga hanyoyin shaye-shaye da sace-sace ko kuma hadaka dai kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Matsalar yin garkuwa da mutane da satan shanu na daga cikin matsalolin da rashin ayyukan yi kan haifar
A wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka, Dr Bawa Abdullahi Wase, ya ce rashin aikin da masana’antu fama da shi a yankin arewacin Najeriya, na daga cikin ababan da suka haddasa matsalar satan shanu a yankin.
Domin jin karin bayani kan muhimmancin wannan rana wacce aka yi mata take a wannan shekara da “koyar da sana’oi domin samarwa matasa abin yi.” Saurari rahoton da Babangida Jibril ya aiko mana daga Legas: