Taron sauyin yanayi na shekara-shekara na Bonn wani bangare ne na tsarin da kasashen duniya ke tantance irin ci gaban da aka samu wajen mutunta yarjejeniyar Paris ta 2015, kokarin duniya na hana yanayin zafi a duniya sama da digiri 1.5 a ma'aunin celcius.
Sakataran Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi Simon Stiell, a cikin wata sanarwa ya ce. "Wannan atisaye ne da aka yi niyya don tabbatar da cewa kowanne bangare ya ci gaba da gudanar da alkawarin da ya dauka, tare da sanin inda aka dosa da kuma yadda za a hanzarta matsawa don cimma manufofin yarjejeniyar Paris."
Duk da haka, Stiell ya yi gargadin cewa binciken zai kasance mai ma'ana ne kawai idan har an dauki matakan da suka dace.
Tsarin da ke kwashe shekaru biyu na faruwa sau daya a kowacce shekaru biyar, kamar yadda yarjejeniyar Paris ta tsara. Yana da sassa uku: tsarin tattara bayanai da lokacin shirye-shirye, kima na fasaha da kuma la'akari da abubuwan da tsarin ya haifar.
Za a kammala hada-hadar shirin ne a watan Nuwamba, lokacin da ake gudanar da taron sauyin yanayi na Amurka (COP28) na shekara-shekara a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa.