Shahararren kamfanin kera kwamfutoci na duniya Microsoft, ya bayyana cewar zai sayi kamfanin kera manhajoji na GitHub, akan kudi dalar Amurka billiyan $7.5 wanda hakan zai kawo karshen rashin jituwa tsakanin kamfanonin biyu.
Kamfanin dake da matsugunni a jihar Washington ta Amurka, ya shahara wajen samar da manhajoji masu kwararran matakai da tsaro, wanda satar bayanai zaiyi wuya a duk wata manhajar su.
Kamfanin na GitHub da aka kirkira a shekarar 2008 yana baiwa kamfanonin damar sarrafa manhajojin su wajen ganin sunyi dai-daito da tsarin kamfanin, ya zuwa yanzu kamfanin na da abokan hulda da suka kai kamfanoni milliyan 28 a fadin duniya.
Hadakar kamfanonin biyu zata samar da tsari mai nagarta da tsaro a duk wata manhaja da suka kirkira, kana zasu samar da damammaki ga ma’abota amfani da manhajojin su.
Facebook Forum