Masu taimakama alkali yanke hukunci da ake kira “Jury” a turance sun cimma matsaya da cewar kamfanin Samsung zai biya kamfanin Apple tarar kudi dalar Amurka milliyan dari biyar da talatin da tara $539.
A dalilin satar fasaha da kamfanin yayi akan wayar sa wadda suka saci wasu tsare-tsare da kamfanin na Apple yayi ma wayar sa, Samsung ya saci tsarin don ya jawo hankalin mutane su sayi wayar sa.
A jiya aka yanke shari’ar da aka fara tun a shekarar 2011, wadda kamfanin Apple yaki yadda da cewar kamfanin na Samsung shine kamfani na daya a duniya da ya shahara wajen kera wayoyin zamani.
Hukuncin da aka dauka a baya, ya bayyana cewar Samsung ya saci fasahar Apple, amma babu wata tara da ta biyo baya, taron wasu masu taimakama alkali a shekarar 2012 sun kara samun kamfanin da laifin satar fasaha, inda suka nemi kamfanin na Samsung ya biya kamfanin Apple dala billiyan daya da rabi.
Amma alkali Lucy Koh, ya rage tarar zuwa dalla milliyan dari biyar da arba’in da takwas, rikicin dai har ya kaiga kotun koli wadda ta nemi da a sake rage adadin tarar, ganin cewar matsalar satar bayanan bai shafi yawan adadin kudin shiga da kamfanin na kasar Koria ta kudu ya samu ba.
Facebook Forum