Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Gear Box Da Injin Mota 75,000 Na Cike Da Fargaba


Fara amfani da motocin da ake kira electric cars ya jefa kimani kamfanoni 75,000 masu kera injinan motoci da gearbox cikin hadarin yuwuwar rasa ayyukan su.

A wata kididdiga da kungiyar cinikayya da kamfanin motocin kasar Jamus yayi, ya nuna cewa kamfanin motocin ya bada ayyuka 840,000 a Jamus, inda 210,00 daga cikin su ne suke kirkira powertrain a cewar Mr Fraunhofar na makarantar kimiyya da fasaha.

Ya kara da cewa ‘yan siyasa da kamfononi suna da bukatar kirkiro sababbin hanyoyin da zasu shawo kan lamarin wannan sauyi.

Mr Joerg Hofmann, yace Kamfanoni dole su kirkiro sabbabin hanyoyin kara koyawa ma’aikata sababbin fasahohi su kuma ‘yan siyasa gyara tsarin daukar ma’aikata aiki.

Wannan barazanar rasa ayyuka 75,000 za a fuskance ta akan kididdigar da akayi a shekara ta 2030, kashi 25% a cikin motoci zasu zama electric cars, 15% hybrids, sai kuma 60% masu amfani da man fetur. Kuma ana sa ran idan har mutane sun cikagaba da amfani da electric cars to kimanin mutane 100,000 ne zasu rasa ayyukan su.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG