Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Apple Ya Gyarawa Matasa Hanyar Hira Da Mutane 32 A Lokaci Guda


Kamfanin wayar hannu Apple, na kasar Amurka ya bada wata sabuwar sanarwa ta bunkasa manhajar faceTme, wadda masu amfani da wayar ke amfani da ita wajan Magana da juna kuma suna iya ganin fuskokin juna a lokaci guda.

Apple ya bayyana cewa yanzu mai amfani da wayar zai iya Magana da mutane 32 a lokaci guda kuma dukkan su zasu iya ganin fuskokin juna a lokacin da suke zantawa.

Manhajar na aiki ne ta yadda duk wanda ya fara Magana hoton fuskar sa zai kara girma, kuma a kowane lokaci ana iya samun karuwar wadanda ke son shiga cikin hirar musamman idan basu kai 32.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG