Trump-wanda har yanzu bai amince da shan kaye a 2020 ba-ya samu nasarar komawa kan karagar mulkin Amurka a zaben daya gudana ranar 5 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Biden ya shigo sahun tsirarun shugabannin Amurka da suka mika mulki ga mutanen da suka rigasu shiga fadar White House-inda hakan ta taba faruwa sa’ilin da shugaba Benjamin Harrison ya mika mulki ga Grover Cleveland a karni na 19.
Dan jam’iyyar Democrat din zai gana da Trump a ofishin shugaban Amurka (Oval Office) da misalin karfe 11 na safe agogon kasar (karfe 4 agogon GMT), kamar yadda fadar White House ta bayyana a Asabar din da ta gabata, inda lokaci ke kara karatowa na komawar tsohon shugaban kasar kan karagar mulki a watan Janairu mai zuwa.
Dandalin Mu Tattauna