Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Za Ta Taimakawa Najeriya Wajen Cike Gibin Da Ake Samu Na Jinsin Mata A Aikin Soji


Wata soja a Najeriya
Wata soja a Najeriya

MDD ta ce, shigar mata cikin gwagwarmayar a matakai daban daban zai taimaka wajen karfafa rundunar soji, don haka majalisar dinkin duniya za ta ci gaba da marawa Gwamnatin Najeriya a kokarinta na cike gibin da ake samu na jinsin mata a aikin soji.

Mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ce ta bayyana hakan yayin wani taro na ganin yadda za a dama da mata a aikin soja.

Amina Mohammed
Amina Mohammed

Mataimakiyar jagoran majalisar dinkin duniyar ta ce suna yabawa gwamnatin Najeriya wajen karfafawa mata gwiwa su ke shiga aikin soja.

Najeriya a cewarta, kamar sauran kasashe, na fama da kalubalen tsaro iri-iri da kuma a cikinsa galibi mata da kananan yara ne su ka fi dandana kudar su.

Don haka sojojin Najeriya na da gagarumar rawar da za su taka don maganin aukuwar ricici da ma kawo karshensa idan ya faru.

Wasu sojoji mata
Wasu sojoji mata

Taron dai da hedkwatar tsaron Najeriya ta shirya da nufin inganta tare da karfafa rawar da mata ke takawa a gidan soja ya sami halartar manyan baki da dama.

Wasu sojojin Najeriya
Wasu sojojin Najeriya

Babban hafsan tsaron kasar, Janaral Christopher Musa ya yi bayanin cewa jigon taron shi ne gina hanyar shigo da mata cikin shawo kan matsalolin tsaro, an yi hakan ne da nufin fuskantar hakikanin abin da ke akwai wajen damawa da jinsin mata da su ne su ka fi yawa.

Hakan a cewar Janar CG Musa zai baiwa rundunar sojin damar tsarawa, aiwatarwa, sa ido da kuma harsashen irin hobbasan da mata ke iya yi a fagen daga da ma bangaren gudanarwa da hakan ka iya karfafa rawar da matan ke takawa wajen shawo kan matsalar tsaro a kasar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG