Ana amfani da sinadarin wajen badda sawu a fagen yaki,amma kuma yana da saurin kama wuta, kuma yana iya kona fatar dan'adam har kashi.
"A wannan lokaci bamu sami wani rahoto na amfani da makamin "white Phsphorus ba" inji kakakin ma'aikatar ta Pentagon komanda Sean Robertson.
Rahoton da Rashan ta bayar yace Amurka ta auna mayakan sakai na ISIS ne kusa da wani kauye da ake kira Hajin. Rasha tace makamin yayi sanadiyyar tashin wuta mai tsanani, amma tace babu rahotannin ko akwai wadanda harin ya rutsa da su.
Yarjejeniyoyin da aka cimma a Geneva, sun haramta amfani da makain na "white phosphorus" kan farar hula ko wasu cibiyoyin soja ko yaki muddin akwai farar hula kusa da wurin.
Facebook Forum