Tallafin ya kunshi, kayakin wanke hannaye wanda aka raba wa kananan hukumomi guda 20 a jihar, da kuma makarantu da sauran wuraren da mutane ke taruwa.
Wakilin UNICEF, Mr. David Damian, a jawabinsa a wajen taron mika kayakin tallafin ya ce, bisa la’akari da irin kokarin da gwamnatin jihar Bauchi ke yi, yasa UNICEF ta bada tallafin.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Bauchi, Dr. Aliyu Muhammed Maigoro, ya ce, tallafin zai taimaka matuka wajen kokarin da suke yi akan yaki da cutar coronavirus.
Babban Sakatare na hukumar samar da tsabtataccen ruwa da muhalli, RUWASA a jihar Bauchi, Alhaji Garba Magaji Babaji, ya shaida ma wakilin Muryar Amurka cewar, kayakin za a yi amfani da su kamar yadda hukumar UNICEF ta tsara.
Ga Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:
Facebook Forum